A ranar Talatar nan ne jami’an tsaro suka kama wasu mutane uku da ake zargin sun sace wayar hannu a kofar shiga harabar wajen taron jam’iyyar APC na kasa.
Wadanda ake zargin sanye da tufafi sun yi amfani da hayaniyar da aka yi a kofar dandalin Eagle Square, inda suka dauki wayar daga aljihun dan jarida.
Dan jaridar da aka sakaya sunansa, ya an karar ne bayan ya gano wayarsa ta bace, lamarin da ya ja hankalin jami’an tsaro, inda suka garzaya wurin da lamarin ya faru.
Sai dai ba a iya gano wayar da ta bace ba ko da bayan bincike da aka yi kan mutanen ukun, saboda sun jefa wayar a karkashin wata motar jami’an tsaro da ke kusa da wurin.
Sai dai wani jami’in ya ceto lamarin ya hango wayar a karkashin motar, lamarin da ya sa aka kama wadanda ake zargin.
Wani dan sanda da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, za a kai wadanda ake zargin zuwa wani ofishin da ke kusa domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.
A watan Maris ne jami’an tsaro suka kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi ne a babban taron jam’iyyar APC na kasa a Abuja.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wasu ‘yan bindiga guda goma a babban taron jam’iyyar PDP a babban filin wasa na kasa a ranar 28 ga watan Mayu.
(NAN)