A jamhuriyar Nijar wasu ƴan gudun hijira da suka tsere daga yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto, sakamakon tashin hankalin ƴan bindiga wanda suka yada zango a garin Abalak a jihar Tahoua na cikin mawuyacin hali.
Ƴan gudun hijirar da suka haɗa da mata da ƙananan yara, na rayuwa cikin wahala inda matan sai sun yi bara suke samun abin da za su ci, watarana kuma su kwana da yunwa.
Kawo yanzu dai babu cikakkiyar ƙididdiga ta yawan mutanen da suka tsere daga yankunansu suka shiga Nijar sakamakon matsalar tsaron.
Bayanai dai na cewa mutanen yankin sun kashe fiye da Naira miliyan 160 wajen biyan kuɗin fansa da harajin da ƴan bindigar ke ɗora musu.
Tun dai bayan kisan Sarkin Gobir, ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka a yankin, inda rahotanni ke cewa sun kama mutm fiye da 160 daga kisan sarkin kawo yanzu. Im ji BBC.