fidelitybank

Ƴan Isra’ila da a ka fara saki sun koma gida

Date:

Hukumomin sojin Isra’ila sun tabbatar da cewa mata ukun nan da Hamas ta saki a cikin ‘yan ƙasar da ta yi garkuwa da su, yanzu sun koma Isra’ila daga Gaza.

A ɗazu ne Hamas ta danka matan ga ƙungiyar agaji ta duniya ta Red Cross, inda ‘yan Isra’ila da dama suka yi maraba tare da murna da sakin nasu, wanda suka kalla ta wani babban allon talabijin da aka girke a babban birnin Isra’ilar Tel Aviv.

Bayan an duba lafiyarsu da da farko daga nan za a tafi da su wani asibiti a kusa da babban birnin kafin kuma daga bisani a haɗa su da iyalansu.

An tabbatar da matan su ne waɗanda Hamas ta bayar da sunansu a waɗanda za ta fara saki – Doron Steinbrecher, da Romi Gonen da kuma Emily Damari.

Kakakin sojin Isra’ila Daniel Hagari a wani taron manema labarai ya ce a cikin wannan mako shida na farko za a rika sakin mutum uku ko hudu duk mako cikin wadanda Hamas ɗin ta yi garkuwa da su.

Wani jami’in Hamas ɗin ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a ranar Asabar za a yi musayar fursunonin ta gaba

Akwai ƙarin mutum 30 da Hamas ɗin za ta saki, rukuni-rukuni a cikin mako shida inda za a riƙa musayarsu da ɗaruruwan Falasɗinawa da ke gidajen yarin Isra’ila.

Motocin Red Cross

Asalin hoton,Reuters

A yau ɗin ne kuma yayin da Hamas ke sakin ‘yan Isra’ilar uku aka ga motocin safa-safa na Red Cross a wajen gidan yari na Ofer da ke yankin Gabar Yamma da Isra’ila ta mamaye, sun je domin ɗaukar fursunoni Falasɗinawa.

Hamas ta ce a duk mutum ɗaya da ta saki na Isra’ila za a saki Falasɗinawa 30 fursunoni daga gidan yarin Isra’ila.

A ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 me Hamas ta kai wa Isra’ila wani harin bazata inda ta kashe kusan mutum 1,200 ta kuma yi garkuwa da 251 da ta kai Gaza. A cewar BBC.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp