Jumillar ‘yan Ukraine 2,437,000 ne suka tsallaka cikin maƙociyarsu Poland tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da yaƙi a ƙasar, a cewar jami’an tsaro na iyakar Poland a yau Asabar.
Sai dai adadin masu tsallakawar ya ragu matuƙa yayin da aka samu adadi mafi ƙaranci a jiya Juma’a tun bayan fara yaƙin a 24 ga watan Fabarairu.
A gefe guda kuma, adadi mai yawa na mutanen na komawa cikin Ukraine, mutum 421,000 ne suka koma ta kan iyakar Poland, in ji hukumar.
A ranar Juma’a kaɗai, 15,000 ne suka tsallaka zuwa Ukraine daga Poland.
Jumillar mutum fiye da miliyan 10 ne suka tsere wa yaƙin a Ukraine, a cewar kwamashinan ‘yan gudun hijira na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).
An yi hasashen cewa ba ya ga miliyan huɗu da suka shiga sauran maƙotan ƙasashe, akwai miliyan shida da rabi da ke gudun hijira a cikin Ukraine ɗin. In ji BBC.