fidelitybank

Ƴan fashin banki sun ci karen su ba babbaka tare da harbe jami’an tsaro a Ekiti

Date:

Wani mumunan fashin banki da aka yi a garin Ikere Ekiti na jihar Ekiti a ranar Laraba da yamma, rahotanni sun ce an kashe mutane biyar ciki har da jami’an tsaro biyu na Amotekun.

An samu labarin cewa ‘yan fashin da suka sanya abin rufe fuska, sun afkawa bankunan kasuwanci da ke kan babbar hanyar garin inda suka bude wuta domin shiga harabar bankunan.

Shedun gani da ido sun ce ‘yan fashin sun ajiye kansu a wurare masu mahimmanci inda suka yi harbi ba kakkautawa har na tsawon sa’a guda, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi a tsakanin mazauna yankin.

Wasu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun samu harbin bindigar ‘yan fashin ne a lokacin da suke kokarin tserewa zuwa tsira.a

Ƴan fashin da suka rufe fuska, kimanin ashirin, sun shiga garin ne da misalin karfe 4:15 na yamma inda suka yi wa bankunan Odo Oja da Oke-osun fashi a lokaci guda.

Kamar yadda majiyar ta bayyana, sun fara kai hari ne kan kwamandan Ikere na Amotekun Corps da ke kan titin Ise, inda aka ce sun harbe wasu jami’an tsaro kafin su far wa bankunan.

‘Yan fashi da makami sun karya kofofin tsaron bankunan da taimakon dynamite, inda suka yi awon gaba da wasu makudan kudade da ba a tantance ba.

Sai dai kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti, Sunday Abutu ya kasa samunsa har zuwa lokacin wannan rahoton, saboda ba a amsa kiran waya da sakonnin wayar salula da dama. In ji Daily Post.

A halin da ake ciki kuma, a wata tattaunawa ta wayar tarho, Ogoga na Ikere Ekiti, Oba Adejimi Alagbado ya bayyana kaduwarsa game da lamarin fashin.

Ya ce abin takaici ne ‘yan fashi da makami sun gudanar da aikin na tsawon mintuna da dama ba tare da wata tangarda ba, inda suka tsere duk da kasancewar shingayen binciken sojoji da rundunar ‘yan sanda a garin.

Oba Alagbado ya ce ya tattauna da jami’an tsaro kan lamarin, kuma dole ne a kama wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp