A jiya ne dai aka samu tashin hankali a unguwar Setillite Town da ke jihar Legas bayan da wasu ‘yan kasar China suka hana ‘yan sanda rufe kamfanin nasu duk da umarnin kotu na yin hakan.
Kamfanin mai lamba 194, Marwa Close, Ijegun Water Site, ana zarginsa da kera fitilun AKT na bogi.
Wani dan kasuwa Ugochukwu Amadi ya kai karar kamfanin a gaban mai shari’a Taiwo Taiwo na wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zarginsa da kera da shigo da fitilun AKT na bogi. Wanda kotu ta bayar da umarni a rufe kamfanin.