Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta bayar da umarnin rufe wani kamfani na kasar China, Golden Tripod Company, sakamakon gurbacewar iskar Carbon monoxide da yake fitar wa a jihar.
An gurfanar da Manajan Daraktan Kamfanin, Mista Lin Zi, da manajan tallace-tallace, Mista Peter Yuan, kamar yadda Blueprint ta bayyana.
An tattaro cewa, an kama mutanen biyu tare da tsare su a ranar Alhamis, sannan daga bisani aka gurfanar da su a gaban kotu a ranar Juma’a, sakamakon harin da ma’aikatansu suka kai wa jami’an gwamnatin jihar.
Kamfanin Golden Tripod da ke cikin babban birnin Uyo yana samar da birki na kekuna masu kafa uku da babura ta hanyar amfani da aluminum, kuma ayyukansa suna gurbata muhalli a koyaushe da carbon monoxide.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya rawaito cewa, an samu tashin hankali a cikin babban birnin Uyo a ranar Alhamis din da ta gabata yayin da ma’aikatan kamfanin suka kai hari kan ma’aikatar muhalli da daukacin tawagar kwamitin kula da muhalli na majalisar da duwatsu da kwalabe a lokacin da suka ziyarci wurin.