Janar Lucky Irabor, Babban Hafsan Tsaro (CDS), ya bayyana cewa akalla ‘yan ta’addar Boko Haram 51,828 da iyalansu sun mika wuya ga gwamnatin tarayyar Najeriya tsakanin Yuli 2021 zuwa Mayu 2022.
Irabor ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da lacca mai taken “Manufar Tsaro ta Kasa da Tsarin Adalci na Wucin Gaggawa a Yaki da Ta’addanci a Najeriya” a bikin ranar kafa Jami’ar Jihar Edo karo na 7, Uzairue, a karamar hukumar Etsako ta Yamma ranar Asabar.
Karanta Wannan:Tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Abacha Oladipo Diya ya mutu
CDS ya kuma ce, tubabbun ‘yan ta’addan Boko Haram 1,543 ne suka yaye a sansanin Mallam Sidi da ke Gombe tsakanin shekarar 2016 zuwa 2022.
Irabor ya ce, “Tsakanin Yuli 2021 zuwa Mayu 2022 kadai, a kalla ‘yan Boko Haram 51,828 da danginsu sun mika wuya, daga cikinsu 13,360 mayakan ne.”