Wani hari da ‘yan bindiga suka kai a tsakiyar yankin Mopti da ke Mali ya yi sanadin mutuwar fararen hula aƙalla 21 da kuma raunata wasu da dama.
Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa wasu ‘yan bindiga ne suka afka kauyen Yarou, sannan suka bude wuta.
Babu wata kungiya da kawo yanzu ta ɗauki alhakin harin.
Rashin tsaro da tashe-tashen hankali sun addabi arewaci da kuma tsakiyar Mali, inda ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke da alaƙa da Alƙa’ida da ISIS ke yawan kai hare-hare. A cewar BBC.