Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun auka Fadar Sarkin Kagarko a kudancin Kaduna, Alhaji Sa’ad Abubakar, inda suka yi awon gaba da ƴaƴansa tara da jikoki da kuma karin mutum uku a garin.
Jaridar Daily Trust ta rawaito wani mazaunin garin, na cewa ƴan bindigar sun kutsa yankin ne cikin dare kamar ƙarfe 11:15 na dare inda kuma suka nufi fadar Sarkin.
“Sun kuma tafi da amaryar sarkin da yaransa tara da jikokinsa amma matar ta kuɓuta, inda ta dawo gida,” in ji shi.
A cewar mazaunin, ƴan bindigar sun kuma yi garkuwa da karin mutum uku ciki har da wata mata, tare da raunata wani Audu Kwakulu na Unguwar Pah wanda a halin yanzu yake samun kulawa a asibiti.
“Ƴan bindigar sun kuma kashe wani makiyayi a ƙauyen Kuchimi tare da sace kaya a shaguna bakwai a kauyen Janjala duka a karamar hukumar Kagarko – a hanyarsu ta komawa,” kamar yadda majiyar ta bayyana.
Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna, DSP Muhammed Jalige bai amsa kiran da BBC ta yi masa game da wannan labari ba.
Kaduna dai ɗaya ce daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro a ƙasar.
Ƴan bindiga sun sha kai hare-hare a sassa daban daban na jihar, yayin da gwamnati ta sha yin alƙawarin magance matsalar.