Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne da ke addabar sassan jihar Ribas, sun kashe wani jami’in ‘yan sanda DPO mai suna Bako Amgbanshin.
DAILY POST ta tattaro cewa, lamarin ya faru ne a daren Juma’a a karamar hukumar Ahoada ta Gabas.
An ce maharan sun yi wa DPO kwanton bauna ne da mutanensa a lokacin da suke wani samame na kai farmaki kan wasu maboyar ‘yan ta’adda a yankin Ahoada ta Gabas.
‘Yan sandan sun yi artabu da ‘yan ta’addan ne da bindiga kafin a kama DPO din, suka kashe shi tare da tarwatsa gawarsa.


