fidelitybank

Ƴan bindiga sun sace mutane 10 a Zamfara

Date:

An yi garkuwa da al’ummar kauyen Matusji fiye da 10 a karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.

Daga cikin wadanda abin ya shafa har da majiyyaci.

Wani magidanci mai suna Ahmad Babangida ya shaidawa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun afkawa al’umma da manyan makamai inda suka fara harbe-harbe kai tsaye da misalin karfe 2:30 na daren ranar Juma’a.

“Dukkanmu muna barci amma tsananin karar harbin bindigar ya tashe mu kuma kowa ya fara gudu”, in ji shi.

Ya ce ko da yake babu wanda ya rasa ransa a harin, amma ‘yan bindigar sun tafi da mutane da dama zuwa inda ba a san inda suke ba.

“’Yan fashin ba su ce komai ba dangane da batun kudin fansa. Ba mu san inda mutanenmu suke ba,” in ji shi.

A cewarsa, wadanda aka sace sun hada da majinyaci da ke karbar magani yayin da yake kan diga IV, yana mai nuni da cewa mutanen kauyen ba su farfaɗo ba daga fargabar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazeed Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 10.

Ya kuma kara da cewa, rundunar ‘yan sandan ta baza jami’an ‘yan sanda masu dabara domin kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su tare da cafke ‘yan fashin.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp