fidelitybank

Ƴan bindiga sun sace Malaman Coci 2 a Katsina

Date:

Rahotanni daga jihar Katsina. na cewa wasu ‘yan bindiga sun afka wa cocin Saint Patrick Catholic Church, da ke Gidan Maikambo, a karamar hukumar Kafur, tare da sace malaman coci guda biyu da wasu yara biyu.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai na cocin Christopher Omotosho ya aike wa manema labarai da jaridar Premium Times ta samu, ya tabbatar da wannan labari .

Jaridar ta ambato shi ya na cewa: “Da tsakar dare ne ‘yan bindigar suka afka wa cocin, suka yi awon-gaba da babban limamin cocin Rabaran Stephen Ojapa, da mataimakinsa Oliver Okpara da wasu yara maza biyu da ke tare da su,sai dai kawo yanzu, ‘yan bindigar ba su kira iyalai ko cocin katolikar ba domin bukatar wani abu’’.

Mr Omotosho ya yi kira ga jama’a su sanya malaman cocin a addu’ar Allah ya kubutar da su.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isa, sai dai bai amsa kiran da wayar salula muka yi masa ba.

www.punch news.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Duk wani tuggun ku Atiku da El-Rufa’i ba za ku iya kayar da Tinubu ba – Bwala

Fadar shugaban kasa ta yi watsi da kokarin da...

Mutuwar Dantata ta girgiza kasa baki daya – Tinubu

Shugaban kasa Ahmad Bola Tinubu ya bayyana Alhaji Aminu...

Wike ya caccaki Rotimi a kan jam’iyyar ADC

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon...

Tsige ni daga mukamin Wazirin Gaya ba a kan doka ba ne – Usman Alhaji

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji, ya...

Gini mai bene uku ya danne Mutane a jihar Legas

Wani gini mai bene uku ya rufta a unguwar...

Kotu ta daure Matashi dan Tiktok da ya ke sanya rigar mama

Wata kotu a jihar Kano, ta yanke wa wani...

Peter Obi ka gaggauta ficewa daga jam’iyyar mu nan da awa 48 – Labour Party

Bangaren jam’iyyar Labour da Julius Abure ke jagoranta, ya...

Lakurawa sun kashe Mutane 15 a Sokoto

Wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Lakurawa ne sun...

Dan wasan Liverpool Diago Jota da Kaninsa sun mu a hadarin mota

Ɗan wasan ƙwallon ƙafar Liverpool kuma ɗan ƙasar Portugal,...

Mun shirya tunkarar APC a 2027 – ADC

A ranar Laraba ne manyan ƴan adawar siyasa suka...

Mun dagulawa Iran lisafi na tsawon shekaru biyu a nukiliyar ta – Amurka

Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce bayannan leken asirinta ya...

INEC za ta fitar da sabbin ƙa’idojin duba sakamakon zaɓe

A shirye-shiryen da take yi gabanin babban zaɓen Najeriya...
X whatsapp