Kungiyar Kudancin Kaduna (SOKAPU) ta yi Allah wadai da sace Hakimin Garu Kurama da wasu ’yan kabilar Gurzan Kurama guda shida a karamar hukumar Kauru ta Jihar Kaduna a daren Juma’a.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Josiah Yusuf Abraks ya fitar, ya bayyana sunayen wadanda aka sacen da suka hada da Yakubu Jadi (Hakimin gundumar), Iliya Yakubu, Nehemiah Tanko, Thomas Tanko, diyar Yakubu Jadi da kuma Cocin Katolika na al’ummar yankin.
SOKAPU ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici, abin tsoro da damuwa.
A cewar sanarwar, “SOKAPU tana kira ga hukumomin tsaro da hukumomin da abin ya shafa da su yi iya kokarinsu don ganin an sako hakimin gundumar Mista Yakubu Jadi da sauran mutane biyar cikin gaggawa.”
Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Hakazalika kungiyar ta yi kira ga al’umma da su kara taka tsan-tsan tare da lura da yadda ba a saba gani ba, da kuma motsin da ba a saba gani ba a yankunansu, inda ta shawarce su da su kai rahoto ga hukumomin da suka dace.