Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan sarkin Fadan Ayu, da ke karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da karamin dansa, Sahabi Halidu Ibrahim.
Sakataren majalisar sarkin, Jibril Adamu Muhammed, ya shaida wa manema labarai cewa ga dukkan alamu maharan suna harin basaraken ne, saboda kai tsaye da suka shiga gidan dakinsa suka nufa suna harba bindiga.
‘Yan bindigar sun yi ta harbi amma kuma Allah ya kare basaraken, a don haka ne suka tafi dansa in ji sakataren.
Jibril Adamu, ya ce, bayan sun fice daga gidan tare da dan basaraken, sun kira waya inda mahaifiyar yaron ta dauka amma suka ce ba za su yi magana da ita ba sai da mahaifin.
Har yanzu dai ana dakon kiran ‘yan bindigar don jin yadda za a yi wajen ceto dan.