Ɗaliban jami’a na gwamnatin tarayya da ke Dutsinma na jihar Katsina huɗu ne ƴanbindiga suka sace a wata unguwar da ake kira da Paris Quarters da ke jihar, wadda take arewa maso yammacin ƙasar.
Mazaunin yankin ne suka tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin, inda suka ce maharan sun isa unguwar ne da misalin ƙarfe 2:20 na daren Asabar, inda suka yi awon gaba da ɗaliban guda huɗu zuwa inda ba a tantance ba.
Mutanen yankin sun ce jami’an tsaron sun zo wajen bayan ƴanbindigar sun riga sun tafi da ɗaliban da suka sace.