An kashe sojoji uku da ƴan sa kai biyu a wani hari da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai a ƙaramar hukumar Toto ta jihar Nasarawa.
Kwamishinan ayyuka na musamman na tsaro da ke jihar, Timothy Kasuwa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa mutane biyar sun rasa rayukansu a lamarin.
“Gaskiya ne sun kashe sojoji uku da ‘yan sa kai biyu,” in ji kwamishinan.“
“Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi musu kwanton bauna a lokacin da sojojin suka je aikin share fage yayin da suke dawowa”
“Lamarin dai ya lafa, sojoji sun kara ƙarfafa jami’ansu da ke kewayen yankin.”
Da yake bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaro yankin domin dakile tabarbarewar doka da oda, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta dauki nauyin lamarin tare da yin ƙoƙarin shawo kan lamarin.