Rundunar sojin Najeriya ta Operation UDO KA ta ce, an kashe jami’ai guda biyu a wani shingen bincike a kan hanyar Umuahia-Owerri da ke jihar Abia.
Wata sanarwa da Laftanar Kanar Jonah Unukhalu na rundunar ya fitar, ya ce lamarin ya afku ne ranar Laraba, inda ya ce suna zargin ƴan awaren Biafra da kuma takwarorinsu na ESN da kai harin.
Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce dakarun sun samu nasarar daƙile harin da aka kai, abin ya sa wasu daga cikin maharan suka tsere da raunuka har da barin motocinsu a wurin.
“Abin takaici shi ne yayin artabu da waɗanda suka kai harin, sojojin mu biyu suka mutu,” in ji sanarwar sojojin.
Wannan shi ne hari na biyu kan shingen binciken sojoji a jihar ta Abia, tun bayan wanda ya lakume rayukan sojoji biyar a watan Mayu.