fidelitybank

Ƴan bindiga sun kashe sojoji 11 a Kaduna

Date:

Kimanin sojoji 11 sun rasa rayukansu yayin wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani sansanin sojojin Najeriya a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda jaridar TheCable ta wallafa.

Daruruwan ‘yan bindigan sun isa sansanin ne a kusa da kauyen Polwire a jiya Litinin kuma sun dauki wani lokaci suna musayar wuta da sojojin da ke cikin barikin.

Wata majiya daga rundunar soji Najeriya na cewa, ‘yan bindigan sun isa sansanin ne bisa babura dauke da manyan makamai, ciki har da bindiga mai harba gurnati.

Majiyar ta ce, an shafe sa’a biyu ana gwabzawa kafin ‘yan bindigan suka iya korar sojojin daga cikin sansanin.

“Mun rasa sojoji 11 kuma an raunata 19 yayin harin. Maharan sun kuma kona wasu motoci masu sulke uku bayan da suka mamaye sansanin”, inji wani jami’in sojojin Najeriya.

Majiyar ta kuma ce, maharan sun kwashe makamai masu dama daga sansanin.

An kai sojojin da aka raunata zuwa babban asibitin Birnin Gwari da asibitin sojojin sama, yayin da aka kai gawarwakin wadanda suka mutu zuwa asibitin 44 da ke birnin Kaduna.

Sai dai ba a sami jin ta bakin kakakin rundunar sojin Najeriya Onyema Nwachukwu ba, kan halin da ake ciki a yankin na Birnin Gwari bayan wannan mummunan harin.

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp