Kimanin sa’o’i 24 da ‘yan bindiga suka kashe mutane 56 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Bakura ta jihar Zamfara, wasu ‘yan bindiga sun sake kashe wasu mutane bakwai a karamar hukumar Maradun ta jihar.
Kananan hukumomin Maradun da Bakura sun raba kan iyaka.
A sabon harin da aka kai da yammacin ranar Asabar, wata majiya a Maradun ta ce, an kai hari kauyuka biyu Faru da Kauyen Minane.
“Ina babban asibitin Maradun lokacin da sojoji suka kawo gawarwakin wadanda aka kashe,” in ji Jamilu Muhammad.
“Mutanen mu da ke kauyen Garin Minane sun ce ‘yan bindigar sun kai farmaki garin ne da misalin karfe 2 na rana inda suka fara harbe-harbe kai tsaye. Abin da suka saba yi shi ne gida-gida don neman dabbobin gida ko wasu kayayyaki masu daraja amma a jiya da suka shiga kauyen sai suka fara harbe-harbe ba da dadewa ba,” inji shi.
A cewarsa, an kashe mutane shida a Garin Minane yayin da aka kashe daya a Faru. Ya ce adadin wadanda aka kashe na iya karuwa saboda da yawa sun bace a kauyukan da lamarin ya shafa.