‘Yan bindiga sun kashe a kalla mutum 23 a wasu tagwayen hare-hare da suka kai wasu ƙauyukan jihar Plateau, a wani rikici mai alaƙa da manoma da makiyaya.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Alfred Alabo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kashe wasu makiyaya biyu tare da manoma 21 a wasu tagwayen hare-hare na ramuwar gayya da aka ƙaddamar a wasu ƙauyukan jihar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya ce ya kaɗu da kashe-kashen, yana mai cewa ya damu matuƙa yadda harkokin tsaron jihar ke ƙara zama abin tayar da hankali.
“Matsalar tsaron jiharmu ya zama tamkar tsohon injin da ke buƙatar kwaskwarima da ingantaccen gyara”, in ji sanarwar.
Jihar Plateau wadda ke tsakiyar Najeriya a lokuta da dama na fama da rikice-rikice masu alaƙa da addini da ƙabilanci


