fidelitybank

Ƴan bindiga sun kashe mutane 18 a Binuwai

Date:

Mutum aƙalla 18 ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da ‘yan bindiga suka kai a yankin Ukohol na Ƙaramar Hukumar Guma da ke Jihar Binuwai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito mai bai wa shugaban karamar hukumar shawara kan harkar tsaro Christopher Waku na cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin Alhamis lokacin da mutane suke tsaka da cin kasuwa a yankin.

Ya kuma ce ana ci gaba da bincike domin gano wadanda suka ɓata.

Shi ma shugaban karamar hukumar, Mike Ubah, ya tabattar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan bindigar sun je wurin ne sanye da baƙaken kaya, kuma da isarsu suka buɗe wa mutane wuta a cikin kasuwar, inda nan take 10 suka mutu.

Ubah ya kara da cewa bayan haka sun kai hare-hare a kauyuka da ke kusa tare da kashe mutum takwas.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Binuwai, SP Catherine Anene, ta tabbatar da kai harin amma ta ce ba su da wasu bayanai ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton

nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp