Akalla mutane 13 ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kashe a wasu hare-hare da suka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Al’ummomin da abin ya shafa sun hada da Kadaddaba, Rafin Gero, da Babban Baye, dukkansu a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Muhammadu Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar harin ga gidan talabijin na Channels, ya ce, an kashe mutane 13 a wasu hare-haren da aka kai a yammacin ranar Alhamis.
Sai dai mazauna yankin sun dage cewa, an kashe mutane 15 yayin harin.