fidelitybank

Ƴan bindiga sun kashe mana dakaru 4 a Katsina – Janar Edward

Date:

Rundunar sojin kasar nan ta tabbatar da mutuwar dakarunta a harin da ‘yanbindiga suka kai wa sansaninsu da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
Tun da farko rahotonni sun ce maharan sun auka wa sansanin rundunar Operation Hadarin Daji ne a ranar Lahadi, inda suka kashe sojoji biyar tare da raunata wasu 11.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust kisan, amma ya ce huɗu ne, ba biyar ba kamar yadda aka ruwaito tun da farko.
Ya ce, A ranar 12 ga watan Mayu, dakarun Hadarin Daji suka gamu da kwanton ɓauna biyu a ƙauyen Kuran Mota da kuma kusa da Alikere da ke ƙauyen Yarmalimai na jihar Zamfara.
Ya ƙara da cewa, duk da dakarun sun yi bakin ƙoƙarinsu wajen kare kansu, abin baƙin ciki an kashe sojoji huɗu daga cikinsu, kuma aka jikkata uku a harin farko.
Ya kuma, a hari na biyu kuwa, sojoji biyar ne suka jikkata sakamakon harbin bindiga, kuma an ba su kulawar da ta dace bayan kai su garin Faskari.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp