Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan jami’an hukumar shige da fice a karamar hukumar Birniwa da ke jihar Jigawa.
Shugaban hukumar reshen jihar, ACG Ismail Abba Aliyu, wanda ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudanar a Dutse babban birnin jihar, ya ce ‘yan bindigar sun kashe jami’insu guda daya sannan suka jikkata mutum biyu.
Ya yi ikirarin cewa, maharan sun yi wa ma’aikansa kwanton-bauna a yayin da suke sintiri a hanyar Galadi zuwa Birniwa, yana mai cewa an kai harin ne ranar Talata da daddare.
A cewarsa, ‘yan bindigar, wadanda suka kai biyar, sun isa wurin da ma’aikatan shige da ficen ke aiki ne a kan babura sannan suka bude musu wuta.
ACG Aliyu ya bayyana cewa jami’in da aka kashe shi ne Abdullahi Mohammed, yana mai karawa da cewa jami’an da aka jikkata su ne Abba Musa Kiyawa da Zubairu Garba.


