Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai wa jami’an hukumar tsaron NSCDC hari tare da kwace makamai biyu a Enugu.
Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, a rukunin gidaje na WTC da ke unguwar Ogui New layout a jihar.
Rahotanni sun ce, harin ya yi sanadin jikkata ma’aikatan, inda ‘yan bindigar suka yi awon gaba da bindigoginsu.
An kai jami’an da suka samu raunuka zuwa wani asibiti da ke kusa, inda a yanzu haka suke samun kulawa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Enugu, Denny Manuel Iwuchukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an da suka jikkata a harin na kwance a asibiti a halin yanzu.


