Rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta tabbatar da mutuwar Gbenga Ogbara, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Atakumosa ta Gabas ta tsakiya.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yemisi Opalola, an harbe jigon na jam’iyyar APC ne a dakinsa da sanyin safiyar ranar Litinin.
Lamarin ya faru ne a garin Igangan, mahaifar marigayi Ogbara.
“Wasu ‘yan bindiga ne suka kashe shugaban APC da misalin karfe 12 na safe. An tura ‘yan sanda yankin,” inji ta.
Opalola ya kuma bayyana cewa ana binciken kisan.