fidelitybank

Ƴan Bindiga sun hallaka Ƴan Sanda uku a Edo

Date:

A ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka kashe jami’an ‘yan sanda uku da jikkata wani guda ɗaya a wani hari da suka kai a jihar Edo.

Bayanai sun ce jami’an bakin aiki ne lokacin da aka yi musu kwanton ɓauna a kusa da garin Agor, kan hanyar Igarra zuwa Auchi na jihar ta Edo.

Rahotanni sun ce an kashe ɗaya daga cikin maharan da jikkata wani daga cikinsu.

An ruwaito cewa an ƙwato bindigogi shida daga hannun maharan.

Lamarin ya faru ne tsakanin karfe 5:30 zuwa 6 na safe kusa da babbar kasuwar Agor.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ta Edo, SP Chidi Nwabuzor, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu cikakken bayani kan harin ba, amma suna ci gaba da bincike

www.nnn.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Na so komawa Manchester United a 2012 – Lwandowski

Ɗanwasan gaban ƙungiyar Barcelona ta Spain, Robert Lewandowski ya...

Isak ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gaba Alexander Isak ya nace sai ya bar...

Sadiq Umar da Bello El-Rufai sun sayi ƙungiyar Ranchers Bees ta Kaduna

Ɗanwasan tawagar Super Eagles ta Najeriya da Real Socieded...

Atiku zai iya guduwa daga ADC ya koma PDP idan Jonathan ya tsaya takara – Diran

Tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa,...

Zoben matar Ronaldo ya kai dala miliyan 5 – Masana

Masana sun yi kiyasin tsadar zoben da Cristiano Ronaldo...

Kama Tambuwal ya na da alaka da shigarsa cikin hadakar jam’iyya – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce kama...

Ambaliyar ruwa ta kashe mutuane takwas a Ebonyi

Ambaliya, wadda mamakon ruwan sama ya janyo, ta yi...

Bankin Duniya zai kashe wa yankin Arewa a Najeriya dala miliyan 300

Bankin Duniya ya amince da kasafin kuɗi dala miliyan...

Giyar mulki na kwasar Trump – ‘Yan Majalisar Democrat

'Yan Democrats a Amurka sun zargi Donald Trump da...

Kama Aminu Waziri Tambuwal da EFCC ta yi ba daidai ba ne – PDP

Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da...

An kai hari a ƙauyuka 15 na Zamfara a mako ɗaya – Rahoto

Wani rahoto da tashar Channels ta ruwaito daga cibiyar Zamfara Circle...

Jihohin Arewa huɗu ne suke biyan mafi ƙarancin fansho na N32,000 – NUP

Ƙungiyar ƴan fansho na arewacin Najeriya, NUP ta ce...
X whatsapp