Jihar Katsina ta sake shiga wani sabon firgici yayin da wasu ‘yan bindiga suka kaddamar da hare-hare daban-daban, inda suka jefa kauyen Goda da unguwar Daudawa cikin wani hali.
Rahotanni sun nuna cewa a daren Lahadi ne kauyen Goda da ke kusa da kan iyakar karamar hukumar Kurfi ya zama cibiyar wani mummunan hari da wasu mahara dauke da makamai suka kai.
Harin ya yi sanadiyar mutuwar wani dan kauyen, a daidai lokacin da aka kona gidaje da dama ciki har da gidan Sagir Goda, wani dan banga a unguwar.
Wani mazaunin Goda ya ce: “Abin ya kasance kamar mafarki mai ban tsoro.”
“Bindigu, gidaje sun kone. Dukanmu mun gudu don ceton rayukanmu. Mun yi rashin makwabci, kuma iyalai da yawa yanzu ba su da gidaje,” inji shi.
A cikin kimanin sa’o’i hudu wasu gungun ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Daudawa da ke karamar hukumar Faskari.
Wani dan unguwar mai suna Alhaji Sale, shi ne ya dauki nauyin harin yayin da masu laifin suka yi awon gaba da shi tare da matansa guda biyu wadanda aka bayyana sunayensu da Amina da Rabi.
“Mun ji karar harbe-harbe da misalin karfe 1:30 na safe,” in ji wani ganau na yankin.
Majiyar ta ci gaba da cewa, “Daga baya, mun gano cewa an dira gidan Alhaji Sale, inda suka tafi da shi, da matansa, da shanunsa guda uku.
“Mun firgita. Wadannan hare-haren suna faruwa akai-akai. Muna kira ga hukumomi da su gaggauta kamo wadannan miyagu tare da dawo da zaman lafiya a cikin al’ummarmu,” in ji wani mazaunin garin.