Rahotanni sun ce, wata kungiyar ‘yan aware mai suna Biafra Nations League (BnL), ta kai hari kan wasu ma’aikatan mai guda biyar da ke kan hanyarsu ta zuwa aiki a safiyar ranar Asabar a Abana, tsohuwar hedikwatar Bakassi.
Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa mayakan masu fafutukar kafa kasar Biafra sun kuma kona kwale-kwalen na ma’aikatan amma ba su iya tabbatar da ko an samu asarar rayuka ba.
Sai dai an samu labarin cewa jami’an tsaron Najeriya sun samu nasarar dakile ‘yan ta’addan a kusa da iyakar Ikang da Kamaru a yankin Bakassi na jihar Kuros Riba, sa’o’i bayan da suka tsere daga bangaren da Kamaru ke iko da shi.
Rahotanni sun ce mayakan sun yi sa’ar tserewa daga kama su da jami’an Najeriya suka yi.
A kwanakin baya ne dai sojojin Kamaru suka mamaye sansanin ‘yan ta’addar amma ba su iya kama ko daya daga cikinsu ba.
Rundunar sojin Najeriya ta kasa tabbatar da faruwar lamarin.


