Dubban ƴan Bangladesh ne suka garzaya zuwa babbar tashar jirgin kasa ta Dhaka da tashohin jiragen ruwa, domin komawa garuruwansu na asali, don bukukuwan Sallah.
Bayan shekaru biyu na matakan korona, ƴan ƙasar na farin cikin dawo da sufuri wanda zai ba su damar zuwa gida cikin sauƙi. A bara an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa don hana mutane ketare iyakokin jihohi saboda tsoron yaɗuwar korona.
Ɗaruruwan ƴan ƙasar ne ke ficewa Dhaka babban birnin Bangladesh a motoci da jirgin ruwa da na ƙasa zuwa ƙauyukansa domin bikin Sallah.