Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida, ya ja hankalin ‘yan kasa a kan su nemi taimakon Ubangiji (SWT) a kan dukkan wasu lamurran siyasar kasar.
Babangida, ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Minna babban birnin jihar Neja, a wani bangare na bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
A cikin jawaban nasa, tsohon shugaban kasar, ya bukaci ‘yan Najeriya a kan su ci gaba yin amanna a kan hadin kan kasa, sannan kuma su sanya a ransu cewa komai zai daidaita da sannu a hankali.
Ya ce “Ina rokonku a kan ku rinka hakuri da juna, kuma ku ci gaba da addu’a don neman daukin Ubangiji a game da wasu lamurra da suka shafi al’muran rayuwa da kuma siyasa.”
Tsohon shugaban na Najeriya, ya ce akwai bukatar a ci gaba da wayar da kan jama’a a kan yadda za su zauna lafiya da juna da kuma samun ci gaba mai dorewa.
Ya kuma shawarci ‘yan jarida a kan su goyi bayan yunkurin da ake na hada kan kasa.
Ya ce, idan har ‘yan jarida za suyi watsi da masu yada jita-jita, to ko shakka ba bu za su samu hanyoyin isar da sakonninsu yadda ya dace.
Kuna abin da ya dace wajen kokarin hada kan kasa da ma sauya al’ummar Najeriya, in ji shi. In ji BBC.


