fidelitybank

Ƙwanƙwasiyya tamkar wata ƙungiyar asiri ce – Kwankwaso

Date:

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana tafiyar siyasar Kwankwasiyya da yake jagoranta cewa, tamkar wata ƙungiyar asiri ce, saboda yadda take kara samun tagomashi a kowane lokaci.

Sanata Kwankwaso, wanda ya bayyana haka yayin hira ta musamman da gidan talabijin na Trust TV. Ya kuma yi ikirarin cewa, Kwankwasiyyar ita ce take jan ragamar siyasar jam’iyyu a Jihar Kano a yanzu.

Ya ce, ’yan siyasar da suka yi fice da wadanda suke cikin tafiyar, lokaci na zuwa da dukkansu za su sake hadewa a karkashin inuwar Kwankwasiyyar “Saboda muna karfafa ta, sannan mun kafa tubalinmu tun daga tushe, wanda hakan yana sosa ran ’yan siyasa da dama.”

“Yadda muke aiki a tsarin Kwankwasiyya ya sha bamban sosai, saboda mun yi amanna da gina mutane.

Daga 1999 zuwa yanzu, babu mahalukin da zai ga adadin wadanda suka ci gajiyar tafiyar Kwankwasiyya, sai lokacin da zabe ya zo ne kadai za ka iya sanin adadin mutanen,” inji shi.

Tsohon Gwamnan, wanda ya ce Jam’iyyar PDP ce ta lashe zaben Gwamnan Jihar Kano a 2019, inda ya kara da cewa, saboda wasu dalilai na jam’iyyar da ma tafiyar Kwankwasiyyar suka yanke shawarar bin lamarin cikin ruwan sanyi.

Ya ce: “Abin da muke yi a yanzu shi ne sake daura damara sannan mu tabbatar duk wanda ya ci zabe a badi an ba shi kujerarsa.

“Haka kuma, ina mai tabbatar maka dan Kwankwsiyya zai yi nasara a zaben.”

Sai dai tsohon Gwamnan ya ja kunnen jam’iyyun PDP da APC cewa lallai ne su sake lale a tsaretsarensu, ya na mai cewa, yadda manyan jam’iyyun siyasar biyu suke tafiyar da al’amuransu akwai bukatar gyara.

Ko da yake Kwankwaso ya nuna cewa zuwa yanzu dai ba ya magana da kowa a Jam’iyyar APC kan yiwuwar sauya sheka zuwa jam’iyyar. A cewar Aminiya.

Sai dai ba zai fid da ran shiga sabon tsarin tafiyar siyasar nan da ake ta magana a kansa na raba-gardama ba, ya na mai cewa, komai na iya faruwa, saboda ya fara tuntuba game da batun.

sun newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp