fidelitybank

Ƙungiyar tuntuɓa ta arewa ta buƙaci a biya diyyar waɗanda aka kashe a Filato

Date:

Ƙungiyar tuntuɓa ta arewa wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta bayyana rashin jin daɗinta kan hare-haren da ke faruwa a jihar Filato ta arewacin Najeriya, inda a kwanakin baya aka kashe mutane da dama, ciki har da ƙananan yara da mata.

A wata sanarwa da sakataren watsa labarai na ƙungiyar, Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta-ɓaci a yankunan da ke fama da hare-haren na ƴanbindiga.

“A bayyana yake mutanen jihar na cikin tsananin tashin hankali, wanda kuma ya zo a daidai lokacin da rayuwa ta yi tsada. Dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashen nan, sannan dole a tabbatar an dawo da zaman lafiya a jihar,” in ji ƙungiyar, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

Ƙungiyar ta kuma yi kira da a ƙara ƙaimi wajen tattara bayanan sirri, sannan a ƙara ƙarfafa jami’an tsaro wajen bibiya tare da kama masu laifi, “sannan su yi bincike domin a hukunta waɗanda aka samu da laifi.”

Haka kuma ACF ta buƙaci a tabbatar da biyan diyya ga wadanda suka rasa ƴanuwansu, sannan a tallafa wa waɗanda suka jikkata.

A ƙarshe ƙungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohi su ƙarfafa malaman addini da masu riƙe da sarautun gargajiya da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki domin taimakawa wajen sulhunta ɓangarori.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp