Kungiyar Tarayyar Afirka, AU, ta zama mamba ta dindindin a G-20 da ake kira Group of 20.
Firayim Ministan Indiya, Narendra Modi ne ya sanar da hakan a yau Asabar yayin da yake bude taron shugabannin a New Delhi, babban birnin Indiya na kasashe mafiya arziki a duniya.
A yayin jawabin bude taron, firaministan Indiya ya gayyaci shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, Azali Assoumani, da ya hau kujerarsa a matsayin mamba na dindindin a kungiyar.
A cikin jawabinsa na bude taron, Modi ya ce “a yau, a matsayinsa na shugaban G-20, Indiya ta yi kira ga duniya da ta taru don sauya gibin amana a duniya zuwa aminci da dogaro.”
“Wannan ne lokacin da dukan mu za mu matsa tare. Ya zama rarrabuwar kawuna tsakanin Arewa da Kudu, tazarar da ke tsakanin Gabas da Yamma, sarrafa abinci da man fetur, ta’addanci, tsaro ta yanar gizo, lafiya, makamashi ko tsaro na ruwa, dole ne mu nemo mafita ga wannan al’umma masu zuwa.”
Kafin taron, G-20 wani taro ne da ya kunshi kasashe 19 da suka hada da Tarayyar Turai.
Rukunin na 20 yana aiki don magance manyan batutuwan da suka shafi tattalin arzikin duniya, kamar kwanciyar hankali na kudi na kasa da kasa, rage sauyin yanayi da ci gaba mai dorewa.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bar kasar zuwa Indiya ranar Talata gabanin taron.


