fidelitybank

Ƙungiyar Malamai ta NUT ta karrama Gwamnoni 6 harda na Kano

Date:

Ƙungiyar Malamai ta ƙasa NUT, ta kararrama wasu gwamnonin ƙasar nan shida kan abin da kira ‘ƙoƙarinsu bunƙasa harkokin ilimi a jihohinsu.

An gudanar da bikin karramawar ranar Asabar a Abuja, babban binrin ƙasar, lokacin da ƙungiyar ta gudanar da bikin ‘Ranar Malamai da Duniya’.

Gwamnonin da aka karrama a lokacin bikin sun haɗa da na Kano, Abba Kabir Yusuf, da na Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, da na Oyo, Seyi Makinde da na Benue, Hyacinth Alia da na Enugu, Peter Mbah da kuma gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris.

Shugaban ƙungiyar NUT na ƙasa, Comrade Titus Ambe, ya ce an zaɓo gwamnonin ne la’akari da irin ƙoƙarinsu wajen bunƙasa fannin ilimi a jihohinsu, musamman tallafa wa malamai da samar da abubuwan ci gaba a fannin koyo da koyarwa a jihohinsu.

Cikin wata sanarwa da sakataren ya ɗa labaran gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf – wanda ya yi jawabi a madadin sauran takwarorinsa gwamnonin shida, ya jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da bai wa fannin bunƙasa ilimi fifiko, saboda muhimmancinsa wajen ci gaban yara masu tasowa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnan tarayya, Sanata George Akume ya yaba wa gwamnonin bisa jajircewarsu wajen bunƙasa fannin ilimi a jihohinsu.

nigeria news today 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp