fidelitybank

Ƙungiyar ma’aikatan Jinya da Ungozoma za su tsunduma yajin aikin Ƙwadago

Date:

Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa, ta ce , mambobinta za su shiga yajin aikin da ake shirin yi a fadin kasar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa na yajin aiki na dindindin a fadin kasar mai dauke da sa hannun sakataren ta T. A. Shettima da shugaban kasa Nnachi Michael Ekuma da mataimakin shugaban kasa Shehu Abubakar da dai sauransu.

“Za ku iya tunawa gwamnatin tarayya ta sanar da cire tallafin man fetur a lokacin rantsar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, a watan Mayun 2023,” in ji wasikar.

Matakin da shugaban kasar ya dauka ya gamu da cikas ga ma’aikatan Najeriya da marasa galihu.

“Shugabannin NLC sun sanya bukatu da yawa a matsayin hanyar da za ta rage wa ma’aikatan Najeriya wahala ba tare da samun nasara ba.

“Shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya sun kaddamar da ayyuka da dama, tun daga zanga-zangar kin jinin gwamnati, yajin aikin gargadi na kwanaki 3, har ma da wa’adin kwanaki 3, amma har yanzu gwamnatin tarayya ta yi kunnen uwar shegu da gargadin kungiyar NLC.

“Saboda haka, shugabannin kungiyar Kwadago ta Najeriya sun yi taro a ranar Talata 26 ga Satumba, 2023 inda suka yanke shawarar fara yajin aikin sai baba-ta-gani.

“Bisa abubuwan da ke sama, an umarce ni da in gabatar da shawarar da kungiyar kwadago ta kasa NLC ta yanke na fara ayyukan masana’antu na kasa baki daya daga ranar Talata 3 ga Oktoba.”

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kare Ya Kashe Ragon Layya: Mai ƙwacen waya ya kashe Sojin ruwa a Kaduna

Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan...

Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram da dama

Da sanyin safiyar ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai...

Tarzomar kama baƙin haure a Amurka na yamutsa hazo

An shiga rana ta uku a tarzomar da ake...

Alhazai sun kammala aikin Hajji bana

A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan...

Tinubu gyaran ƙasa za ka mayar da kai ba zaɓen 2027 ba – ACF

Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya, ta yi kira...

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...
X whatsapp