Kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Zamfara (NBA), ta koka kan kisan daya daga cikin mambobinta Barista Benedict Torngee Azza da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi a Gusau babban birnin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na jiha Barista Junaidu Abubakar ya sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai a Gusau.
A cewar shugaban, ya samu kiran waya daban-daban guda uku a ranar Alhamis 18 ga watan Agusta 2022 daga abokan aikinsa, inda suka sanar da shi cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka harbe Barista Azza, kuma gawarsa na kwance a kan titin Bye-pass kusa da ofishin hukumar FRSC, Gusau. babban birnin jihar.
“Bayan samun labarin, sai na garzaya wurin da lamarin ya faru, inda na hadu da abokan aikinmu, Barista Abdullahi Ibrahim da Barista Ibrahim Sani Gusau tare da jami’an tsaro da dama (’yan sanda da sojoji).


