fidelitybank

Ƙungiyar Gwamnoni ta gana a kan batun Harajin Tinubu

Date:

Ƙungiyar gwamnoni ta ƙasa, ta yi wani taro a cikin dare a hedikwatarta da ke birnin Abuja, inda rahotanni ke cewa sun tattauna abubuwa da dama ciki har da batun ƙudirin dokar haraji da ta janyo cece-ku-ce a ƙasar.

Babu dai bayani daga gwamnonin a kan abin da taron nasu ya cimma wa, amma rahotanni daga jaridun ƙasar sun ce batun ƙudirin dokar harajin ne jigo a zaman gwamnonin na jiya Laraba da daddare.

Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki ne suka fi yawa a taron, inda aƙalla 15 suka halarta, sai gwamnoni biyu daga jam’iyyar Labour da kuma na APGA ɗaya.

Ƙudirin dokar harajin wanda shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar ya janyo suka da ƙorafi daga masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnonin ƙasar a ƙarƙashin majalisar ƙoli ta tattalin arziki, da gwamnoni da ƴan majalisa daga yankin arewa da ma ƙungiyoyi da dama.

Gwamnonin Arewa 19 kuma sun bayyana rashin goyon bayan su ga wasu sassa na ƙudirin, tare da neman a gaggauta janye shi daga majalisar dokokin tarayya.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp