fidelitybank

Ƙungiyar ECOWAS za su gana a Abuja

Date:

Shugabannin ƙungiyar ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas za su gana yau Lahadi a Abuja, domin tattauna batutuwan da suka shafi haɗin kai da tsaro da kuma tattalin arzikin yankin.

Ana sa ran batun ficewar ƙasashen yankin Sahel daga ƙungiyar ne zai zama babban manifar taron na yau.

Ƙa’idar da Ecowas ta gindaya ta sanarwar shekara guda kafin ficewar ƙasa daga ƙungiyar  wanda ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka yi, zai cika a watan Janairu mai zuwa.

A makon da ya gabata ne, shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya shaida wa shugaban Jamus da ya ziyarci ƙasar, Frank-Walter Steinmeier, cewa muradun walwalar ‘yan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar ne babban abin da ke ran shugabannin Ecowas.

Inda ya alƙawarta yi amfani da diplomasiyya da hikima wajen maido da ƙasashen cikin ƙungiyar.

Shugaba Tinubu – wanda shi ne shugaban Ecowas – ya sha amfani da hanyoyin diflomasiyya don ganin ya janyo hankalin ƙasashen na yankin Sahel domin su koma cikin ƙungiyar.

general news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp