Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Jigawa ta yi watsi da tukwicin 10,000 da gwamnatin jihar za ta bai wa ma’aikatanta a matsayin kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Wannan yana kunshe a cikin wata sanarwar da aka saki bayan kammala taron kungiyar da aka yi ranar Talata a Dutse.
Sanarwar wadda shugabannin kananan hukumomi da kuma sakatarorin ƙungiyar ƴan kwadago ta NLC da TUC reshen jihar suka saka hannu ta fasalta yadda gwamnatin ta yi azarɓaɓin yanke hukunci kan bada tukwicin tun da ba su cimma yarjejeniya ba.
A farkon makon nan ne dai gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya amince da biyan ma’aikatan jihar kudi 10,000 a duk wata a tsawon watanni uku, kafin gwamnatin tarayya ta fito da tsarin sabon albashi.
A makon da ya gabata ne dai gwamnatin tarayyar karkashin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin domin yin duba ga albashin da ake biya mafi kankanta a Najeriya.