fidelitybank

Ƙungiyar ƙwadago ta mayar wa da Tinubu martani a kan sabon albashi

Date:

Ƙungiyar kwadago ta NLC ta soki lamirin bayanin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi kan cewa an cimma matsaya game da sabon albashin ma’aikata mafi karanci a ƙasar.

Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma dage kan buƙatarta ta neman sabon mafi karancin albashi na kasa ya kasance naira 250,000.

A yayin da yake jawabi a ranar Laraba, lokacin bikin ranar dimokuradiyya, Tinubu ya ce an cimma matsaya kan batun sabon mafi karancin albashin da aka dade ana muhawara a kai tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago.

Shugaban ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a aika da wani kudirin doka na zartarwa ga majalisar dokokin ƙasar domin ta tsara sabuwar yarjejeniyar mafi karancin albashi.

Sai dai a wata sanarwa da NLC ta fitar a jiya Laraba, muƙaddashin shugaban NLC, Prince Adewale Adeyanju, ya ce babu wata yarjejeniya da kwamitin bangarori uku suka cimma kan batun mafi karancin albashi na kasa a lokacin da aka kammala tattaunawa a ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni, 2024.

Ya ce, “Har yanzu bukatarmu ta mafi ƙarancin albashin ma’aikata na nan a kan naira 250,000, kuma ba a ba mu wasu kwararan dalilai na sauya wannan abu da muka yanke ba”.

Kungiyar ta NLC ta ce ya zama wajibi ta “jawo hankalin shugaba Tinubu da ‘yan Najeriya da masu ruwa da tsaki su sani domin da alama waɗanda suka yi masa bayanin sakamakon tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin uku ba su fada masa hakikanin halin da ake ciki ba”.

Sanarwar ta kara da cewa: “Duk da cewa shugaban kasa ya yi cikakken bayanin wasu sassan tarihin tafiyar dimokuradiyya, a bayyane yake cewa ba a yi masa cikakken bayani game da sakamakon tattaunawar mafi ƙarancin albashi ba.

Ƙungiyar ta ce babu wata yarjejeniya kuma dole ne ta fahimtar da shugaban kasa da ’yan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki na kasa kan hakan.

Al’ummar Najeriya dai sun yi tsammanin ko shugaban ƙasar zai faɗi matsayarsa game da sabon ƙarancin albashin ma’aikata a Najeriyar, wanda aka gaza cimma matsaya tsakanin ƙungiyar ƙwadago da ɓangaren gwamnati a tattaunawar da aka kammala cikin makon da ya gabata.

Yayin da ƙungiyar ƙwadago ta dage kan naira 250,000 a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, ɓangaren gwamnati da ƴan kasuwa sun kafe ne a kan naira 62,000.

Yanzu haka dai ana jiran matakin da ƙungiyar ƙadagon za ta ɗauka bayan ƙarewar wa’adin da ta bayar na samun matsaya kan albashi mafi ƙaranci a ƙasar, wanda yana cikin sharaɗin da ta gindaya gabanin janye yajin aikin da ta fara a ranar Litinin ɗin makon da ya gabata

nigerian news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp