Manyan ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya, NLC da TUC sun buƙaci mambobinsu da su daina aiki daga ranar Talata, yayin da suke shiga yajin aikin na sai-baba-ta-gani a fadin ƙasar duk kuwa da umarnin da kotu ta bayar na hana su yin hakan.
Ƙungiyoyin dai na matsa wa shugaban ƙasar Bola Tinubu ne ya dawo da tallafin man fetur din da aka kwashe shekaru ana amfani da shi a baya, wanda ke sanya farashin man fetur yin rahusa.
Amma gwamnatin ta ce tana la’akari da tabarbarewar tattalin arziƙin ƙasar, tare da shirin karkatar da kudadenta wajen gudanar da ayyukan jin kai.
Ƙungiyoyin dai na son gwamnati ta ƙara mafi karancin albashin ma’aikata zuwa akalla dalar Amurka 120 daga kusan dala 36, tare da sauya wasu manufofinta na tattalin arziki da ba su yi wa talakawa daɗi ba.
Shugaban TUC, Festus Osifo ya bayyana cewa yajin aikin zai ci gaba da tafiya har sai an samu kyakkyawan martani daga gwamnati a dukkan matakai.
Wannan matakin dai ya biyo bayan umarnin dakatar da yajin aikin da wata kotu da ke Abuja ta bayar a baya-bayan nan, koda yake har yanzu babu tabbas kan tsawon lokacin da yajin aikin zai gudana.
Amma ana sa ran zai shafi manyan ayyuka kamar asibitoci da tashoshin jirgin kasa, da makarantu a ƙasar mafi girman tattalin arzikin Afirka.
Kungiyoyin dai sun yi barazanar shiga yajin aikin akalla sau uku tun bayan da Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayu, amma sai aka yi gaggawar dakatar da su bayan ganawar da suka yi da shugaban, lamarin da ya sanya ayar tambaya kan yanke hukuncin nasu.
Ana kuma kallon yajin aikin na ranar Talata a matsayin nuna adawa da harin da aka kai wa shugaban ƙwadagon, Joe Ajaero a jihar Imo a makon da ya gabata.