Kulob din ƙasar Denmark mai buga matakin aji na biyu, Jammerbugt Fodbold Club, ya nada Paul Aigbogun a matsayin sabon kocin kungiyar.
Aigbogun ya kasance tsohon kocin kungiyar ‘yan kasa da shekara 20 ta Najeriya, Flying Eagles.
Dan shekaru 50 ya kasance mataimakin daraktan fasaha na hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) kafin nada shi.
Wannan dai shi ne karo na hudu Aigbogun zai jagoranci kulob a wajen Najeriya, bayan ya yi wasanni a Nevada Wonders da San Francisco Seals da kuma Glacis United.
‘Yan wasan Najeriya takwas yanzu haka suna buga wasa a Jammerbugt FC.
Sun hada da Ahmad Gero, Promise Damala, Shola Collins, Victor Ochay, Solomon Ogberahwe, Abdullahi Garba, Muhammad Ibrahim da Nasiru Jibril.
Kungiyar ta buga wasanninta na gida a filin wasa na Jetsmark mai daukar mutane 6,000 da ke Pandrup a Arewacin Jutland.