Yayin da wa’adin da babban ministan birnin Abuja Nyesom Wike ya bai wa mabarata na daina bara a titunan babban birnin ke cika a Litinin din nan, ƙungiyar masu bukata ta musamman da ke Arewa ta yi kira ga ƴaƴanta da su tashi da azumi a ranar don neman Allah ya kawo masu dauki.
Kungiyar ta kuma nemi masu ruwa da tsaki tun daga kan yan majalisar wakilai, da sanatoci da sarakunan da sauran mahukunta su shiga lamarin.
Shugaban ƙungiyar masu bukata ta musamman na arewacin Najeriyar Yarima Sulaiman Ibrahim, ya shaida wa BBC cewar, ya kamata a ce ministan birnin tarayya Abujan ya sake shawara, duk da cewar abun da ministan ya fada doka ne kuma ba za su hana doka aikinta ba, amma babban matsalar ita ce ministan ya ce akwai wadanda ke sajewa da jama’a suna bayar da bayanan sirri ga bata-gari a cikinsu, don haka wannan ya jefa rayuwarsu cikin barazana, domin zai janyo musu kyama daga wajen jama’a.
A cewarsa “Abun da muke so shi ne a duba wacce dama dokar kasar ta ba mu, sannan a kira mu a tattauna da mu don jin mastaloloinmu, a kira taron gagganwa na masu ruwa da tsaki, a duba a ji me ake yi kan masu baukata ta musamman, a gano dalilan da suke sa mu yin bara. A samar da hanyar dakile wannan mastalar” in ji Yarima.
Talla
Haka kuma ya ce babban abin da suka fi bukata shi ne “ba wai a ɗauki kayan abinci a kai shi wata masarauta ba ne, ko a ba su jari na naira dubu asirin ko duba hamsin ba, ba wannan ne buƙatar mu ba, illa a saurare mu aji koken da muke da shi, a magance mana matsalolinmu” in ji shugaban ƙungiyar.
Haka kuma ya ce akwai dokar da tsohon shugaban Najeriya Muhamamd Buhari ya sa wa hannu kan masu bukata ta musamman, inda aka ware kashi 5 cikin ɗari zuwa sama ga masu bukata ta musamman a kowacce ma’aikata, da ba a aiwatarwa.
Najeria@64: Nakasassu sun koka kan rashin ‘yancin walwala
2 Oktoba 2024
Ba mu san makomarmu ba a cikin gwamnatin Tinubu: in ji masu bukata ta musaman
7 Agusta 2023
Abin zai iya hana naƙasassu bara a Najeriya
17 Yuli 2023
Yarima Sulaiman Ibrahim ya ja haknalin ƴa’ƴan kungiyarsu da su kar su dauki kowane irin mataki, su jira suga sakamakon tattaunawa da zasu da minsitanda sauran amsu ruwa da tsaki kan lamarin tare da tashi da azumi a gobe Litinin din.
Sai dai ya yi kira ga Sanatoci, da ƴan majalisar wakilai, da sarakuna da kungiyar dattawa ta arewa, da Malaman arewacin kasar da su gane cewar su ‘ƴa ‘ƴa ne gare su, idan shar suka bari aka ci zarafinsu, to hakikinsu na kan wuyansu.
Matsalar bara dai matsala ce da ta yiwa yankin arewacin Najeriya katutu, sau da yawa a kan danganta ta da masu bukata ta musamman ko yaran da ake aikawa almajirci daga bisani su bige da neman abinci, sai dai a kashin gaskiya akwai tarin mutanen da rashin abin na kai ke sa su shiga harkar duk da suna gida tare da iyalansu.
Shi yasa wasu ke danganta lamarin da talauci, a ke kuma yin kira ga gwamnati ta tashi tsaye wajen samawa jama’a aikin yi, ko kuma inganta yanayin nema a kasar ta yadda jama’a za su tashi tsaye don neman na kansu.
Yayin da har yanzu ake cigaba da muhawara game da dacewa, ko rashin dacewar gwamnati ta kyale marasa karfi su yi bara, masharhanta na kara jaddada cewa akwai banbanci sosai tsakanin bara, da kuma almajirci, wanda ke nufin neman ilimi.