Majalisar dattawa ta yi wa kudurin shirin rage radadi na gwamnatin Najeriya wato Social Investment Program karatu na biyu da manufar yi wa dokar gyaran fuska.
Daga cikin kwaskwarimar da majalisar da ke son yi wa kudirin dokar shi ne dauke shirin daga ma’aikatar jinkai zuwa ofishin shugaban kasa.
Sanata Mohammed Ali Ndume shi ne mai tsawatarwa a majalisar dattawa ne ya kawo kudirin.