Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana rahotannin da ke kwarmata yiwuwar faɗaɗa ayyukan soji na Isra’ila a zirin Gaza da matuƙar masu tayar da hankali idan har da gaske ne.
Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Miroslav Jenca ya shaida wa taron kwamitin tsaro cewa matakin zai iya haifar da mummunan sakamako ga miliyoyin Falasɗinawa da kuma ƙara jefa rayukan sauran mutanen da aka yi garkuwa da su cikin hatsari.
An kira taron ne bisa buƙatar Isra’ila bayan bayyanar wasu bidiyo da ke nuna biyu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su – cikin mummunan yanayi.