Jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce, ƙofar jam’iyyar a buɗe take ga duk wanda ke da ra’ayin shiga , ciki har da tsohon gwamnan Kaduna Mallam Nasir El-Rufai.
A baya-bayan nan dai an ga wani bidiyo da ke nuna wata ziyara da Sanata Kwankwason ya kai wa tsohon gwamnan na Kadunan a gidansa.
Mallam Nasir El-Rufai dai ya samu saɓani da gwamnan jihar daya gaje shi, Sanata Uba Sani, abin da ya sa wasu ke ganin zai iya ficewa daga jam’iyyarsa ta APC.


