Ministan Abuja, tsohon Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya ce ba zai hana ƴanmajalisar jihar ƙarƙashin jagorancin Martins Amewhule aikinsu da doka ta ba su dama ba.
Haka kuma Wike ya zargi sakataren gwamnatin jihar, Tammy Danagogo da ruruta rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.
Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da ƴan ƙabilar Ijaw a garin Abalama da ke jihar.
Wike ya ce, “na ji wasu na cewa ban isa in zo nan ba. Ina suke yanzu?. Irin wannan tarbar da kuka mini ta nuna cewa abin da ake yaɗawa a kafofin watsa labarai ƙaryar banza ne. Ina godiya kuma zan cigaba da kasancewa tare da ku,” kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wike ya yi godiya ga Shugaban Najeriya Bola Tinubu, wanda a cewarsa ba don ya ba shi muƙamin ba, “da ba mu san wa zai riƙe mutanenmu ba.”