Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymr Zelensky, ya gargadi cewa, nan da wasu sa’o’i kaɗan dakarun Rasha za su dirarwa birnin Kyiv a ƙoƙarin ƙwace ikonta.
A wani jawabi da ya gabatar kai-tsaye zuwa ga ‘yan kasar, Mista Zelensky ya bukaci mutane su ci gaba da nuna jajircewa, ya na mai sanar da cewa, an riga an yanke hukunci kan makomar Ukraine.
A cewar BBC, mazauna birnin Kyiv sun sake shafe wani dare a tashar jirgin kasa na karkashin kasa da duk wani wuri mai ginin karkashin kasa.
Sojojin Ukraine sun ce, a na gwabza kazamin fada a yankin da sojojin Rasha ke kokarin sauka da jirginsu a nan birnin Kyiv din.